YANZU-YANZU: Trump ya yi barazanar kai wa Iran mummunan martani idan ta kai hari Amurka
YANZU-YANZU: Trump ya yi barazanar kai wa Iran mummunan martani idan ta kai hari Amurka
DOMIN SAYAN DATA MAI SAUKI DA ARAHA KU DANNAN DOMIN SAUKE APP DIN
https://play.google.com/store/apps/details?id=forfor.dataap
Donald Trump ya yi wa Iran kashedi a ranar Lahadi, yana mai cewa za ta dandana “cikakken karfi” na dakarun sojin Amurka idan ta kai hari kan Amurka, yana jaddada cewa Washington “bata da wata alaka” da hare-haren da Isra’ila ta kai wa cibiyoyin nukiliya da na leken asiri na Tehran.
A cewar gwamnatin Iran, harin da Isra’ila ta kaddamar tun daga safiyar Juma’a a wuraren nukiliya da na sojin Iran hari, inda mutane da dama suka mutu, ciki har da manyan hafsoshin soji da masana nukiliya.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi alkawarin kai hari “kan kowanne wuri da ke karkashin tsarin mulkin Ayatollah,” yayin da Iran ta mayar da martani da jerin hare-haren makamai masu linzami masu karfin Gaske
Duk da cewa Trump ya ce yana da masaniya game da shirin harin Isra’ila kafin a fara, ya sake nanata a safiyar Lahadi a shafin Truth Social cewa Amurka “bata da hannu a harin da aka kai wa Iran a daren Juma'a.”
“In an kai mana hari ta kowace hanya, iri ko salo daga Iran, za ku dandana cikakken karfi da azabar dakarun sojin Amurka a matakin da ba ku taba gani ba a tarihi,” in ji Trump cikin wani rubutu.
Ya kara da cewa: “Za mu iya cimma yarjejeniya cikin sauki tsakanin Iran da Isra’ila, mu kawo karshen wannan hare-hare!!!”
A ranar Juma’a, shugaban Amurka ya bukaci Tehran da ta shigo teburin sulhu ko kuma ta fuskanci “hare-hare mafi muni” daga Isra’ila.
No comments