Babban Hafsan Sojin Iran ya bayyana cewa an kammala shirin kaddamar da “aikin hukunta” gwamnatin Isra'ila, yana mai cewa hare-haren da Iran ta kai a baya kawai gargadi ne domin hana kai hari nan gaba.
Babban Hafsan Sojin Iran ya bayyana cewa an kammala shirin kaddamar da “aikin hukunta” gwamnatin Isra'ila, yana mai cewa hare-haren da Iran ta kai a baya kawai gargadi ne domin hana kai hari nan gaba.
A cikin wani saƙo na bidiyo da aka fitar da shi a daren Talata, Janar Mai Girma Abdolrahim Mousavi ya ja kunnen gwamnatin Isra'ila da ta shirya domin karɓar hukuncin da Iran za ta aiwatar sakamakon abin da ya kira da harin rashin dalili da Isra’ila ta kai wa Iran.
Kwamandan ya bayyana cewa duk hare-haren da Iran ta kai zuwa yanzu ba su wuce gargadi ba ne, don nuna cewa Iran na da karfin kare kanta, yana mai jaddada cewa zai biyo bayan hakan ne da hukuncin da zai tabbatar da ladabtar da gwamnatin Isra’ila.
Ya kuma fitar da gargadin gaggawar ficewa daga yankuna, inda ya bukaci mazauna yankunan Falasdinu da Isra’ila ta mamaye, musamman mutanen Tel Aviv da Haifa, da su fice daga wadannan wurare don ceton rayukansu, kada su sadaukar da kansu saboda “bukatar Benjamin Netanyahu”.
Ya ce al’ummar Iran ba su taɓa mika wuya ga duk wani hari ko danniya ba a tarihi, kuma wannan karon ma za su fuskanci hare-haren Isra’ila da karfin hali, tare da daukar matakin hukunta gwamnatin israila
Babban kwamandan ya bayyana cewa dakarun Rundunar Sojin Sama ta IRGC da cibiyar kare sararin samaniya, wadanda ke kan gaba a fagen fama, sun samu goyon bayan sauran rundunonin soji daga sojin kasa, IRGC, 'yan sanda da kuma Ma’aikatar Leken Asiri domin fatattakar abokan gaba, inda suka kai munanan hare-hare kan muhimman cibiyoyin Isra’ila.
An bayyana cewa sojojin Iran sun kai jerin hare-haren makamai masu linzami na ramuwar gayya kan Isra’ila tun daga ranar 13 ga Yuni, bayan da gwamnatin Sahyoniyawa ta kai farmaki kan Iran ba tare da wata hujja ba.
Wadannan hare-haren da Isra’ila ta kai sun hada da kai farmaki kan cibiyoyin nukiliya, soji da na fararen hula, wanda ya yi sanadin shahadar manyan hafsoshin soja, masana kimiyyar nukiliya da fararen hula, ciki har da mata da yara guda 45.
Iran ta jaddada cewa wannan aika-aika ba zai wuce haka ba, kuma hukuncin da za ta aiwatar ba zai bar komai ba ga gwamnatin Sahyoniyawa.
No comments