Wani Makami ne Iran ta Jefa shi sararin samaniyar Isra'ila
Wani Makami ne Iran ta Jefa shi sararin samaniyar Isra'ila ?
Ga kaɗan daga cikin bayani akan Makamin Anti-Satellite (ASAT) Strategic Weapon ?
Wani makami ne daga cikin manyan makaman zamani da wasu kasashe masu karfin soja ke amfani da su don kare kansu ko kuma nuna karfin iko a sararin samaniya (space). Ga cikakken bayani game da shi:
MENENE ASAT?
ASAT (Anti-Satellite Weapon
) wani makami ne da ake ƙera shi don ƙona ko lalata tauraron dan adam (satellite) da ke cikin sararin samaniya. Ana iya harba shi daga ƙasa, jirgin sama, ko tauraron dan adam ɗin kansa.
YA AKE SARRAFA MAKMAMIN Direct-Ascent ASAT (DA-ASAT):
Ana harba shi daga doron ƙasa kai tsaye zuwa tauraron dan adam don tarwatsa shi.
Misali: India ta gwada wannan nau'in a shekarar 2019 (Mission Shakti).
Wannan nau’i na ASAT yana hawa sararin samaniya, sai ya nufi tauraron dan adam da zai kai farmaki daga kusa (misali: ya tare shi ko ya harbe shi daga kasa.
MENENE MANUFAR IRAN AKAN WANNAN MAKAMI?
Babban burin Iran shine kwace ikon sararin samaniyar Isra'ila don sarrafa makamanta cikin sauki ga inda take son kaisu.
— Abdul Journalist
No comments