CLICK HERE👇

                        DOWNLOAD APP

Breaking News

Da dumi'dumi: Jam'iyyar APC ta bukaci Zullum da ya gaggauta tuba tare da neman Afuwar Ganduje kan kokarin haɗa Yan dab domin Kai masa hari a wajen taro.

 Da dumi'dumi: Jam'iyyar APC ta bukaci Zullum da ya gaggauta tuba tare da neman Afuwar Ganduje kan kokarin haɗa Yan dab domin Kai masa hari a wajen taro.


Kungiyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta arewa ta tsakiya ta bukaci gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, da ya gaggauta neman afuwa kan zargin hada baki da ‘yan daba wajen kai hari ga kan shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, yayin taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Gabas a Gombe ranar Lahadi.


 Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya jagoranci zanga-zangar hargitsa taron bayan Ganduje da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (Arewa-maso-Gabas), Kwamared Mustapha Salihu, sun amince da Tinubu a karo na biyu ba tare da amincewa da Shettima ba.


An Tilasta fitar da Ganduje da Salihu daga wurin taron cikin tsauraran matakan tsaro yayin da aka yi zanga-zanga a wurin taron.


 Da yake mayar da martani ga wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya fitar a ranar Litinin, kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ta caccaki Zulum, inda ta zarge shi da hada baki a kan shugaban jam’iyyar APC na kasa.


 Kungiyar ta kuma kare matakin da Ganduje ya dauka, inda ta ce shugaban kasa ne kadai zai iya zabar mataimakin shugaban kasa a zaben shugaban kasa.


 Sanarwar ta kara da cewa, “Hakkin shugaban kasa ne ya nada mataimakinsa, ba wanda zai tilasta wa Bola Tinubu ya zabi wanda ya dace ya zama mataimakinsa, ya rage masa ya zabi wanda yake ganin zai iya aiki da shi.



 “Muna yin Allah wadai da matakin da Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya dauka, na hadakar ‘yan daba don su far wa shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Abdullahi Ganduje, Ganduje wanda ba shi da wani laifi, yana gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya tanada a matsayinsa na shugaban jam’iyyar na kasa.

No comments