CLICK HERE👇

                        DOWNLOAD APP

Breaking News

WASU DAGA CIKIN MANYAN CIGABAN KIMIYYA DA FASAHA DA IRAN TA KIRKIRO

 🚀 WASU DAGA CIKIN MANYAN CIGABAN KIMIYYA DA FASAHA DA IRAN TA KIRKIRO


An hana sayar mata kayan aiki, an buga mata sanctions, an hana ta sukuni... amma duk da haka ga wasu daga cikin manyan cigaban da ta kirkiro a cikin gidanta da iliminta na kimiyya da fasaha:



1 — Tana da nuclear technology wanda dalilinsa suka gina Bushehr Nuclear Power Plant, sannan akwai Fordow facility na karkashin kasa mai suna Fordow Fuel Enrichment Plant - shi ne wanda aka fasa dutse aka gina shi a ciki


2 — Ta samar da advanced centrifuges kamar IR-6 da IR-8, wanda abun mamaki ne ga kasa irinta, hakan ya ba wa mutane mamaki


3 — A bangaren space science, ta harba satellites kala-kala zuwa orbit, wanda hakan ya sa ta shiga jerin kasashe kadan wadanda suka tura satellite ba tare da taimakon wata kasa ba


4 — Sun kirkiri dubunnan ballistic missiles kamar Fateh-110, Sejjil, da Khorramshahr, bugu da kari kuma da hypersonic missile wanda ake ganin abun mamakinsa yanzu mai suna Fattah-2 



5 — Akwai manyan drones kamar Shahed-129, Mohajer-6, da Shahed-136 - wanda Russia take amfani da wasu daga cikinsu a yakinta da Ukraine. Wanda ya ba wa Russia kayan aiki ai ba kyal ba ne! 


6 — Iran ce kasa ta farko a Islamic countries da ta fara cloning animals a 2006


7 — Sun samar da COVID-19 vaccine nasu na kansu mai suna COVIran Barekat


8 — A bangaren cyberwarfare suna da manyan facilities nan ma ba a bar su a baya ba, da sauransu


Game da missiles, bari ka ga guda daya daga cikinsu 👇



Fattah-2 shi ne “the most advanced hypersonic ballistic missile” da Iran ta taba kirkira. Yana iya yin tafiyar 1,500km, kuma speed dinsa ya kai 15,000 km/h. Kenan idan suka harba shi zuwa Taabib ba ya wuce 5mins kacal yake isa.


Yana iya dogding interception, saboda haka yake matukar wahala ga missile defense systems su iya kakkabe shi. Asali ma an kirkire shi ne saboda ya zama gwaska yadda babu wani defense sysyem da zai iya kakkabo shi. 


Idan ya tashi kanka to ba kai kadai ba, Western analysts su da kansu abun ya tashi kansu. Sun yi matukar mamaki saboda sun yi tunanin Iran ba za ta iya mallakar hypersonic tech ba sai 2030 zuwa sama, sai kwatsam ta gabatar da shi a 2023. 


Wannan daya kenan, kuma akwai wasu mayu irin su Noor, Qader, Abu Mahdi, Soumar, Hoveyzeh, Sejjil-2, Shahab da sauransu kowanne akwai specific aikinsa.


Malam mutanen nan suna da shiri ka ji. Ba su kwanta bacci ba! Wadanda suke underrating dinsu, su ne abun kallo.


Duk da haka fa suna cikin sanctions gaba da baya, babu wata kyakkyawar diplomacy, babu kwakkwaran hadin-gwiwar aiki, bugu da kari ana binta slowly ana sheke mata masana da kayan aiki.


📌 Bari in rufe da wani quote dinsu:


“If we wait for others to help us, we will be colonized again. But if we suffer and build it ourselves, we will become independent forever.” 


Idan ka karanta ka yi sharing ↗️


Allah Ya fisshe mu. Amin.



Technologist and Scientist


15th June 2025

No comments