CLICK HERE👇

                        DOWNLOAD APP

Breaking News

ME YA SA IRAN BA TA MALLAKI MAKAMIN NUCLEAR BA?

 🚀 ME YA SA IRAN BA TA MALLAKI MAKAMIN NUCLEAR BA?


Abun tambaya ne babba ga abun da ya hana Iran mallakar makamin nuclear har zuwa wannan lokacin. Tambayar da ake ta yi kenan a rubutuna da ya gabata. 


To wadanne dalilai ne? 🤔


Duk da cewa wasu suna ganin already tana da shi kawai boyewa take yi, amma bari mu gani a nan:


Da farko dai ga kadan daga cikin dalilan da ke sa a mallaki makamin nuclear:


1 — Zama superpower - kowacce kasa tana so ta zama superpower, kuma babban abun da ya zama wajibi gare ta shi ne a ji tsoronta (ta zama invulnerable) ta hanyar mallakar manyan muggan makamai. Don haka tun daga 1900 zuwa yau babu wani mugun makami mafi hatsari a doron kasa kamar Nuclear weapon, don haka mallakarsa kamar goga kafada da kafada da manyan kasashen duniya ne



2 — Yaki - an ce ana tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ko? Kamar dai abun da US ta yi wa su Hiroshima wanda ya sa duniya ta ji tsoronta. To duk wanda yake da nuclear weapon ana masa kallon gwaska ne, ba za a tsokane shi a yaki da ganganci ba, kuma idan ma an fara yakin shi ma zai ce bari ya dauko kayan aikinsa... ai kura ta san gidan mai babbar sanda!


3 — Ana amfani da nuclear a non-weaponry use, kamar samar da wutar lantarki da sauransu.


Now, mun san cewa a 1979 aka yi Iranian revolution, to tun kafin wanann lokacin aka ba wa Iran licence na mallakar nuclear (kafin ta zama Islamic republic), amma bayan wannan lokacin sai Ayatullah Ali Khamenei, Supreme Leader na Iran, ya ba da fatawar haramta amfani ko mallakar makamin nuclear! (zan ajiye reference a comment)


Sai suka ajiye lamarin suka shiga kirkirar manyan muggan makamai wadanda muke gani a wajensu yanzu. Kuma wani abun burgewa game da Iran shi ne, ba sa dukawa don a taimake su su gina kasarsu ko makamai a gaban Turawa. Shi ya sa wannan izzar tasu take bakantawa Turawa rai ainun.

Buy data click

To a baya-bayan nan sai suka dawo da lamarin mallakar nuclear saboda yadda duniya ta juya, kuma duba da yadda ake tada hankula a Middle East. Amma a wannan karon kuma sai aka ce musu wai sai sun yi signing deal a 2015, wai su tsagaita wanann kudirin, amma a 2018 Donald Trump ya yi watsi da shi, wanda hakan ya fusata Iran suka ci gaba da aikinsu babu kama hannun yaro.


Kasancewar Iran tana kiran kanta Islamic Republic, sai US, da Europe da su Israel suka buga mata mugun takunkumi cewa ai tana taimaka wa 'yan ta'adda har ma ta kyankyashe wasu, don haka idan ta mallaki nuclear za ta zama babbar barazana ga Middle East gabadaya musamman Israel.


Duk da cewa suna bi a hankali suna kashe mata masana ta bayan fage, amma hakan bai hana Iran ci gaba da aikinta na mallakar nuclear ba. A yanzu haka abun da aka sani shi ne ta mallaki 60% na enriched uranium wanda hakan yake nuna cewa ta kai kaso mai tsoka a mallakar nuclear, tunda bai wuce 10% ya zama makami ba, sai kuma design da sauran abubuwa.


Wannan dalilin ya sa Netanyahuu ya yi mugun tsorata ya tada hankalinsa, babban burinsa shi ne a yi wa Iran taron dangi a hana ta mallakar nuclear. Ya san cewa nan da 'yan watanni Iran za su fara test! Shi ya sa a wannan attack din aka yi targeting nuclear scientists dinsu da facilities.


A zahiri, idan Iran tana da nuclear ba za ta boye ba saboda babu wanda take tsoro. Yanzu tana denying ne kawai tana so sai abun ya zama “murucin kan dutse” tukunna ta sanar cewa ta mallake shi, wanda hakan zai sa Israel ta shiga taitayinta. 


Har zuwa yanzun nan, Iran ba ta sanar cewa tana da makamin nuclear ba. Ba mu sani ba idan zargin da ake mata gaskiya ne, to watakila za su mallaka ne bisa larura. Abun da dai take nunawa shi ne ita threshold nuclear state ce, wato kasar da take da tech, resources, da talent din kera nuclear amma ba ta kera ba. Misali, na iya kuma zan iya yi, amma ba zan yi ba saboda wani dalili ko ra'ayina.


Idan ka fahimta ka yi sharing ga wasu ↗️


Allah Ya musu jagora! 



Technologist and Scientist


14th June 2025

No comments