Idan ya kasance ƙasar ku bata da fasahar "Radar System" to kun zama makafi a kan duk abinda zai faru a sararin samaniyar ku.
Idan ya kasance ƙasar ku bata da fasahar "Radar System" to kun zama makafi a kan duk abinda zai faru a sararin samaniyar ku.
Domin ta amfani da fasahar "Radar System" za'a iya ganin missiles, drones da bibiyar motsin abokan gaba, gargaɗin hukumomi da jama'a don a shirya zuwan hare-hare, shirya harbo makaman da aka aiko da sauransu.
Dole ne sai anyi hack!ng fasahar radar system sannan za'a iya aiko da makamai masu linzami irin su missiles, drones da sauransu a cikin kasa idan har ba'aso kasar ta iya ganin zuwan wadannan makaman masu linzami. Wannan zai gamsar dakai cewa !sra'il sun yi kutse ma Radar system na kasar ir@n.
Idan har haka ne to ya abin yake a nigeria, muna da fasahar "Radar system" ko muma makafi ne a air space namu?
Nigeria tana da wasu ƙananan na'urorin "Radar System" amma ba domin aikin soja ba, domin zirga-zirgar jiragen sama na farar hula, suma ɗin ba gabaɗaya ƙasar bane suke aiki, musamman yankunan karkara (Ƙauyuka), a takaice nigeria ba ta da ingantaccen tsarin kariyar jiragen sama ko makamai masu linzami irin na ƙasashen da suka ci gaba. (Shiyasa nake cewa hawan jirgi a nigeria, kawai Allah ne yake karewa amma akwai haɗari sosai).
Haka zalika ɓangaren cyber defense system na nigeria haryanzu yana kan developing ne, sannan akwai ƙarancin ƙwararru a fannin yaƙi ta yanar gizo (cyberwarfare).
A takaice, Nigeria is vulnerable akan kawo hare-hare daga ko wace kasa ba tare da mun sani ba. kuma cikin ƙanƙanan lokaci za'a iya rusa ƙasar.
NB: Nigeria muna da arziƙin da zamu iya samar da ingantacciyar "Radar System" da Air Defense System" amma matsalar shugabanin mu basa hangen gobe, sunfi yarda da gina manyan gidaje da siyen manyan motoci da makamantansu.
Allah yasa mu dace.
No comments