CLICK HERE👇

                        DOWNLOAD APP

Breaking News

Me Ya Sa Makamin Kariya na Isra’ila Ya Gaza Gano Hare-haren Iran?

 Me Ya Sa Makamin Kariya na Isra’ila Ya Gaza Gano Hare-haren Iran?


Ranar Lahadi da ta gabata, duniya ta shiga dimuwa sakamakon wata gagarumar arangama tsakanin Iran da Isra’ila. Wannan hari ya girgiza kasashen duniya, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda makaman kare dangi na Isra’ila suka kasa gano ko dakile hare-haren da suka fito daga Iran.


Fasahar "MurkyTour" Na Iran 


A cewar wasu rahotanni da ke yawo a kafafen leƙen asiri, ana zargin cewa Iran ta yi amfani da wata sabuwar fasaha da ake kira MurkyTour wajen kai harin da ba a hangowa cikin lokaci ba. Wannan fasaha na iya dusar da ganewar makaman kariya na zamani da suka hada da Iron Dome, tsarin kariya da Isra’ila ke amfani da shi don harbo makamai masu linzami a iska.


Martanin Iran 


A martanin da ta fitar, Hukumar sararin samaniya ta Iran ta musanta yin kutse kai tsaye a cikin na’urorin Isra’ila, amma ta tabbatar da cewa an yi amfani da wata sabuwar fasaha da ba a bayyana cikakken tsarin ta ba. Wannan ya kara jefa duniya cikin rudani, inda masana ke ci gaba da bincike kan irin wannan sabuwar dabarar da Iran ta mallaka.


Isra’ila Na Zargin Kutsen Fasaha


Isra’ila ta bayyana cewa Iran ta kutsa cikin tsarin Iron Dome, wani na'ura mai hankali da ke mallakar Isra’ila amma wanda aka gina da taimakon fasahar Amurka. Wannan kutse ya hana Iron Dome gano makaman da suka nufi wasu muhimman wurare a kasar.



Abin Mamaki Ga Duniya


Harin ya zo a bazata matuka, inda kasashen duniya da dama suka nuna damuwa game da irin kwarewar da Iran ke samu wajen harhada makamai da fasahar kutsen kwamfuta. Haka Zalika harin ya bude tambayoyi game da irin kariyar da Isra’ila ke da ita da kuma yadda Iran ke kara habaka a fannin fasahar zamani. Rahoto daga -abdul journalist

No comments