BALA'IN DA ZAI FARU IDAN AKA HARBA MAKAMIN NUCLEAR!
DOMIN SAYAN DATA MAI SAUKI
👇👇👇👇
Www.forfordata.com.ng
📌 Saboda sanin mugun hatsarin makamin nuclear ne ya sa manyan kasashe suke rikicewa idan suka ji labarin wata kasa tana kokarin mallakarsa, saboda lamarin ba na wasa ba ne.
Sannan mafi yawancinmu kawai muna jin sunan nuclear ne amma ba lallai ba ne idan mun san irin hatsarinsa, bari ka ji dalilin da ya sa Malam Bahaushe ya kira shi da sunan “makamin kare dangi” a wanann misalin da zan bayar na bala'in da zai faru idan aka harba shi.
Misali, gobe Lahadi da asuba, sai Russia (tana da nuclear warheads guda 5,500+), sai ta harba guda daya ga birnin TaAbib, ga abun da zai faru cikin 1-second:
—Nuclear bomb din zai haskaka samarin samaniya fiye da hasken rana
—Nan take duk wanda ya kalli hasken nan zai makance
—Surface temperature na wajen zai haura 10,000°C (duk zafin da ake yi a Sokoto/Maid ba ya wuce 46°C, imagine 10,000 now!)
—Kusan duk wani abu mai rai zai mutu nan take (lamarin da zai kashe mutane sama da 1,000,000)
—Duwatsu, karafuna, bishiyoyi, gine-gine... duk za su fara tafarfasa
—Duk wani gini (ko ya kai Burj Khalifa tsayi) nan take zai rushe
...wannan a cikin 1-second kenan fa.
Bari mu ci gaba. A cikin 1-minute kuma ga abun da zai faru:
—Duk wani flammable abu kamar oil, gas stations, chemicals da sauransu za su kama da wuta
—Sannan su ma ababen hawa, da gidaje, da komai da komai za su kama da wuta
—Mushroom cloud zai tashi har tsayin 20km zuwa sama, sannan ya dawo da gurbatacciyar iska mai dauke da radiation a siffar kura ko hazo
...bari mu sake ganin me zai faru bayan haka:
—Kasar garin za ta lalace kamar girgizar kasa
—Wadanda suka yi saura ba su mutu ba za su fara rashin lafiya kamar cancer, severe injury, amai da gudawa, da sauransu saboda tsananin radiation
—Za a yi tsananin rashin abinci, wuta, da ruwa saboda gabadaya iskar garin da kauyukansa ta gurbace. Wadanda suka rage ba su mutu ba za su koma kamar wasu zombies, sai mutuwa ko ina
Bayan duk wadannan kadan daga cikin abubuwan da za su iya faruwa cikin 24-hours kacal, daga nan kuma mutane da dama ba za su kara haihuwa ba (saboda cututtuka ko gurbacewar DNA), wasu ma ko wata daya ba za su kara yi ba.
Gabadaya birnin zai tashi a aiki. Ba zai zaunu ba, ba za a sha ruwan wajen ba, ba za a yi noma ba, sannan iskar da take kadawa a wajen zuwa wasu wurare su ma abun zai shafe su. Wanann lamari zai ci gaba da wakana har na tsawon watakila shekaru 50 zuwa 70. Climate change activists sai dai ku yi hakuri saboda an jika muku aiki!
Nuclear weapon kala-kala ne. Ga misali da karfinsa:
1 — Hiroshima Bomb - wanda ya kashe mutane 140,000+ a 1945 (wannan tsohon version ne) - nauyinsa ya kai 15 kilotons
2 — Modern Bomb - zai iya shafe New York ko Paris duka, nauyinsa ya kai 1,000+ kilotons
3 — Hydrogen Bomb - zai iya shafe kasa sukutum ko kasashe biyu ko uku, kai har yanki sukutum ya kan iya shafewa a doron kasa - nauyinsa ya kai 50,000+ kilotons - shi ne irin wanda Russia ta yi test a 1961 mai suna Tsar Bomba.
Misalin da na bayar a sama shi ne idan aka harba Modern Bomb. Tun da aka fara amfani da nuclear bomb, sau biyu aka taba harba shi kai-tsaye kan mutane, wato na Hiroshima da Nagasaki a 1945 wanda US ta yi.
Yanzu kun ga dalilin Malam Bahaushe na cewa makamin kare dangi ko?
Kafin in rufe ga jerin kasashen da suke da nuclear da adadinsu:
-Russia - 5,889
-US - 5,244
-China - 500
-France - 290
-UK - 225
-Pakistan - 170
-India - 164
-Israel - 90
-North Korea - 40
Allah Ya kiyaye. Kun ga kenan idan za a yi ta harba su kamar yadda ake harba missiles, ai za a yi wa duniya “reset all” kafin lokacin tashinta ya yi. Amma tabbas Dan-Adam ya kirkiro mugun makami a duniya.
Idan ka fahimta ka yi sharing ga wasu ↗️
No comments