CLICK HERE👇

                        DOWNLOAD APP

Breaking News

Ga yadda za’a farfado da noma a Arewa: darussa daga kasashen duniya

 

Tun shekarun baya, noma ne zuciyar rayuwa a Arewacin Najeriya. Daga gonakin auduga na Funtua zuwa kwandunan tumatir a Kano, da filayen shinkafa a Kebbi — yankinmu yana ciyar da miliyoyin mutane. Amma yanzu manoma na fama da ƙarancin amfanin gona, rashin kasuwa, kayan aiki na da, da kuma rashin tsaro.


Wannan ba lallai ne ya ci gaba da kasancewa haka ba.


Wasu ƙasashe a duniya sun taɓa kasancewa a irin wannan hali — manoma na fama da talauci, babu ci gaba — amma sun gyara tsarin su, sun tashi tsaye, kuma sun samu nasara.


Ga yadda mu ma za mu iya:


1. A Zuba Jari a Kan Manoma — Kamar Yadda Rwanda Ta Yi


Bayan yakin basasa da kisan kare dangi a shekarun 1990, noma a Rwanda ya durƙushe. Amma gwamnati ba kawai gina hanyoyi ta yi ba — ta kuma horar da manoma, ta kafa ƙungiyoyin hadin gwiwa, ta tabbatar da cewa kowane manomi yana da ingantattun iri, takin zamani, da jami’in kula da noma.


Sakamakon haka

Daga 2000 zuwa 2020, amfanin gona a Rwanda ya ninka sau biyu — kuma an rage talauci sosai.


Me Arewacin Najeriya za ta iya yi:

 • A ɗauki ƙwararrun jami’an kula da noma a kowace ƙaramar hukuma

 • A ƙarfafa ƙungiyoyin manoma domin taimako da horo

 • A rage farashin iri da taki ga kananan manoma — ba manyan kamfanoni kawai ba


2. A Yi Amfani da Fasaha Wajen Magance Matsaloli — Kamar India


India ta fuskanci matsanancin yunwa. Amma ta ƙaddamar da Green Revolution, inda aka raba ingantattun iri da na’urorin ban ruwa, sannan aka fara aikawa da saƙonnin wayar salula domin gargadi akan ruwan sama, cututtuka, da farashin kayayyaki.


Yanzu India na fitar da abinci zuwa wasu ƙasashe.


Me Arewacin Najeriya za ta iya yi:

 • A haɗa kai da kamfanonin waya domin aika saƙonnin gargadi akan yanayi a harshen Hausa da Fulfulde

 • A tsaida da farashin kayayyaki kai tsaye daga kasuwa domin a hana yaudara

 • A gwada ban ruwa da hasken rana (solar irrigation) a jihohin da ruwa ke wahala kamar Yobe da Jigawa


3. A Gina Abubuwan Da Manoma Ke Bukata — Kamar Vietnam


Shekarun 1980s, Vietnam na cikin talakawan duniya. Amma yau, su na fitar da shinkafa da borkono zuwa wasu kasashen duniya. Ko me ya sa?

Sun faro daga tushe — hanyoyi, rumbunan adana kayan gona, ruwa, da kuma rance marar riba.


Me Arewacin Najeriya za ta iya yi:

 • A gyara hanyoyin da ke haɗa gona da kasuwa

 • A gina rumbunan ajiya a matakin ƙauye domin rage asarar kayan amfanin gona

 • A ba matasa rancen kayan noma mara ruwa da takura a Zamfara, Katsina, Gombe da sauransu


4. A Kare Manoma Daga Rashin Tsaro — Kamar Colombia


Colombia na fama da rikice-rikice na ’yan bindiga da ’yan fashi. Amma da goyon bayan jama’a da tsauraran matakan tsaro, sun sake dawo da gonakin noma, kuma sun farfado da fitar da kofi ☕️ da koko (Cocoa) zuwa kasashen waje.


Me Arewacin Najeriya ya kamata mu yi:

 • A kafa agro-guards (masu tsaron gona) tare da taimakon jama’a

 • A dawo da filayen noma da ‘yan ta’adda suka hana amfani da su

 • A ƙarfafa sarakunan gargajiya da masu gadi na gida tare da tsari da horo


✊🏾 Lokacin Gyara Yanzu Ne


Sabunta noma a Arewa ba yana nufin mu kwaikwayi wasu ƙasashe ba ne — yana nufin mu koya daga nasarorin su kuma mu daidaita shi da al’adunmu, ƙasarmu, da mutanenmu.


Maganin nan ba yana nesa da mu ba ne. Mu na da dama. Idan muka tashi tsaye — manoma, matasa, shugabanni da jama’a — za mu iya dawo da martabar noma a dan karamin lokaci.


“Ba sai mun yi bara ba id


an muka rungumi noma da ilimi da haɗin kai.”



Karfin Jama’a — Sabuwar Duniya.

#SabuntaNoma #TashiArewa

No comments